Adam a Zango wanda aka fi sani da Prince zango ya shiga wani rudani saboda kwace account dinsa na instagram da yankutse sukayi, wanda wannan account yanada mabiya akalla miliyan daya da rabi, lallai wannan ba karamar asara bane ga jarumin duba da dimbin kudi da account yake kawo masa tareda samun talla kaya na kamfanunka da dama, a yanzu haka jarumin ya bude sabon account na instagram inda ya hakura da dayan.
Jarumai da dama sun nuna alhini ga abinda ya daru da jarumin kuma sun tausaya masa, wasu da dama acikinsu sun taimaka masa wajen tallata masa sabon shafinsa acikin shafukansu. Lallai akwai aiki mai girma a gaban Adam A.Zango na farko kara tara dimbin mabiya wanda abune da zai dauki tsawon lokaci, na biyu samun tantancewa daga kamfanin instagram na uku kuma samun tallace tallace daga manyan kamfanun nuka wanda abune da zaiyi kasa bisa ga hasashen masana a wannan fanni. Allah ya bashi ikon juriya da hakuri.