API

Aisha Aliyu Tsamiya - Ta sami mabiya Miliyan Daya a Instagram

Aisha Aliyu Tsamiya ta shiga sahun masu mabiya miliyan daya (1million Followers) a Kannywood 
Jarumar ta Hausa film industry wato kannywood wacce aka Santa da AISHA ALIYU TSAMIYA ta nuna godiya ga mabiyanta tareda alfahari dasu da irin kauna da suka nuna manata don samun maniya miliyan daya a Instagram, lallai wannan wani baban nasara ne a gareta duba da irin tasirin mabiyan da kuma arziki da hakan zai kawo mata, jarumar itama tana cikin sahun mata jarumai masu saye da sayarwa inda take sayar da abaya kuma hakan zai taimaka mata domin tallata hajarta harma da na wasu da zasu iya biyanta domin ta tallata musu harma da kamfanunnuka na gida da waje. 
masana harkokin sada zumunta da sanin sirrikan na kafafen sun yi nuni ga cewa nasarar jarumar yanada alaka da sanarwa da ta bayar a kwanakin baya a shafin nata na gargadi ga masu tura kudi ta Facebook, inda jarumar tace ita bata da shafin Facebook kuma bata taba budewa ba, duk shafuka masu amfani da sunanta a Facebook na yan damfara ne, don haka kar wani ya tura mata kudi ta Facebook ko saboda chat da akayi ta Facebook da sunan itace don kuwa ba ita bace yan damfara ne, hakan yasa masu yada labarai sun ta yadawa idan labaran yaja hankali sosai duba da irin sura da kyau da Aisha tsamiyan ta kara yi a videon gargadin da ta wallafa, wanda hakan yasa mabiya sun binciki shafin nata sosai domin ta nemi duk mai son yayi magana da ita musamman akan kasuwancinta to ya garzayo Kai tsaye shafinta na Instagram.