Fim din MATI A ZAZZAU ya gama cin kasuwar sa ta sabuwar sinimar zamani dake ginin Ado Bayero Mall... Inda ya karkare kasuwamcin sa a Naira Milyan Hudu da Dubu Dari Takwas da Arbain da Daya da Dari Hudu (N4,841,400). Wannan babbar nasara ce ba karama ba, kasan cewar a sinima daya rak aka haska shi a kewayen Nigeria, amma ya hada wannan makudan kudi da baa taba hada irin su ba tundaga fara haska finafinan Kannywood a sinimar zamani.
Masu hasashe dayawa sunyi hasashen fim din zaikai Milyan Biyar (N5,000,000) sai dai kash ya gaza karasawa... Shin wanne fim kuke tunanin zai karya record din Mati A Zazzau ya fara hada Milyan Biyar a finafinan Kannywood?
Film din MATI A ZAZZAU Yafi kowani film kawo kudi a kannywood Milyan Biyar (N5,000,000)