JARUMA a FILMHOUSE CINEMA KANO
Fim ne irin wanda akewa lakabi da (female oriented film) maana fim din da mace ce zata jaa ragamar sa... Amma duk da haka ya hada manyan kwararrun jarumai da suka hada da ALI NUHU, SHAMSU DAN IYA, SALISU S FULANI, SULEIMAN BOSHO, MUSA MAI SANA'A.
Fim din sati daya kacal zayyi a sinima yana hada kudi, wani fim din zai biyo bayan sa mai taken ZALEEHAT na jarumi ABDUL M. SHERIFF. Ba kamar MATI A ZAZZAU daya samu sati uku yana ta shan sharafin saba.
Nawa kuke tunanin fim din JARUMA zai hada a kwanakin uku na karshen makon nan, kasan cewar sune rana kun da aka fi kaddarawa anfi samun kudi acikin su a bisa al'adar sinima.