Hafsat idirs ta wallafa karin arziki da tayi na sayan motar ne a shafinta na Instagram inda dimbin masoyanta da abokai suka rinka yimata fatan alheri da addu'a ta alheri, yayinda abokan harkarta da dama suka rinka wallafawa suma a shafikansu don tayata murna ciki harda sarki Ali nuhu wanda mutane da dama sukeyi masa kallon amini, mai gida kuma aboki na kut da kut ga Hafsat idris. Ita dai hafsat idris ta taba aure kuma tanada yara da dama kuma lallai kyakykyawace matuka duk da cewa ta taba aure, tanada dimbin masoya da dama tareda mabiya masu yawa kuma jigoce a harkar film na hausa inda ta taka rawa a manya manyan finafinai da ake Ji dasu kamarsu labarina na aminu saira wanda ake sanyawa a tashar arewa 24 da ma sauran fina finan hausa masu tasiri matuka.