API

Breaking News - MAKIYA NA SHIRIN FITAR DA SABON VIDEO NA KAQE DON BATA MIN SUNA - Inji Minister Sheikh Pantami

Ministan sadarwa da tattalin arziki na kimiyya a Nigeria wato Sheikh Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami ya bayyana cewa makiyansa na shirin fidda sabon video domin bata masa suna, Sheikh Pantami a kwanakin nan ya tsinci kansa a wani mawuyacin hali inda wata jarida dake kudancin Nigeria ta fitar da cewa Pantami yana cikin jerin mutanen da kasar amurka ka sa ido a kansu saboda ra'ayin ta'addanci, lamarin da ya tayar da hankali a wannan lokaci, bityo bayan kiranye kiranye da Allah wadai da jama'a sukayi kan kazafin da akayiwa ministan wanda kuma malami ne na islama ya sanya jaridar ta goge labarin daga shafukanta kuma ta fito ta bada hakuri.


Ministan ta bakin kakakinsa Uwa Sulaiman, Pantami yace shirin ya biyo baya ne bayan yunkurin da akayi dan bata mashi suna wajen alakanta shi da boko haram, da basuyi nasara ba shine suke so su bijiro da wani salon, amma duk da haka Pantamin ya shaida cewa bazasu nade hannu su bari arinqa yimusu irin wannan cin fuska ba kuma zai dau mataki bisa doka da oda.
duk da cewa fadar shugaban kasa Buhari ta fito ta wanke Pantami amma hakan bai sa masu kiran a tsige ministan ba kuma suna ta kara matsa lamba da kira akan lallai Pantami ya ajiye mukamin nasa don bada dama ayi masa bincike kan abubuwanda ake zarginsa akai.  a bangare guda kuma jama'a da dama na arewacin Nigeria musamman musulmai da malaman addini na Islam sun kare Pantami inda mafiya yawanci ke cewa kiyayyace kawai ake nuna masa saboda nasarori da ya samu a ma'aikatarsa tareda nasararsa a matsayinsa na malamin Musulunci kuma mai jagoranci a gwamnati ta kasa.