A ranar litinin na watan azumin Ramadan wanda yayi dai dai da 26/4/2021 wuta ta kunno a arewa twitter da suke ma lakabi da street violence.
Shafinmu na twitter wato @kanywoodflix yayi tsananin bincike kan abinda ya kawo rikicin, mun gano @XharaBKumbo ta saki hoto inda ta gargadi maza bunsuraye masu neman mata da suyi hankali kar azuminsu ya karye yayinda suke gallon
Saboda hoton na zahra kan iya janyo wa su rasa azumin nasu, yayinda @_hafsat_paki miniyar zahra ta yaba kawar tata tareda jinjina mata, Kwatsam sai ga game changer tweet na @caramel__queen_ ya shigo, wacce ita maryama ta kasance shahararriya wajen rubutu na Arabic calligraphy, inda ta saki harsashi Mai kibiya biyu take cewa " 1. Wawayen banza da 2. Wofi"
Hakanne ya harzuka @XharaBKumbo
Hakan ya sanya @XharaBKumbo tace in mutum ya isa ya fado suna, kwatsam sai ga 'yan bani na iya da masu sayan rikici ko kyauta ne sun shigo.. Daga Nan Street ya rinchabe.
Ga dai abubuwan da muka tattaro a halin yanzu a kasa
Duk da cewa wuta ta danyi sanyi a street na arewa twitter, yanzu dai fadan ya koma chille chille, daga cikin bayanai da muka samo @XharaBKumbo ta fadi cewa abinda take so ta tabbatar yau gashi @caramel__queen_ ta tabbatar mata, a tweet in Xahra ta bijiro
Xahra ta bijiro maganar tsohon saurayinta, inda a hange na shehunan twitter suke ganin cewa da alama ko tuntuni akwai zargi da ya shafi lamari irin na WUFF🤯 da saurayi a cikin annobar da ta barke, ga dai harsashen da zahran ta saka jim kadan bayan shan ruwa na 26/4/21
Zahra ta wallafa "Someone should send this to Caramel Queen: 3 months kenan ina jiran evidence and finally you tweeted it today by yourself, I swear I’ll never allow you to go free for all the fabricating stories you’ve been spreading about me both you and my Ex must pay"
Bisa yanda bayanai ke zuwa mana daga shehunan twitter na arewa, rikicin da ya barke a yau cikin street zai iya kaiwa ga kotu, kamar yanda hakan ta faru a lokutan baya da wani celebrity wato rikicin deezell da maryam booth.