API

History - Tarihin Hadiza Aliyu Gabon

Cikakken tarihi ingantacce akan fitacciyar jaruma a masana'antar fina finan Hausa wato Kannywood, wannan jaruma yar asalin kasar Gabon ce kuma sunanta Hadiza Aliyu Gabon.

  
Hadiza Aliyu ta shiga kannywood ba da dadewa ba bayan ta shigo daga Gabon zuwa jihar Adamawa, Najeriya . Ta tashi daga Adamawa zuwa Kaduna yayin da take sha'awar shiga masana'antar fim ta kannywood tare da dan uwan ta.

 
Ta samu damar ganawa da Ali Nuhu kuma ta nemi taimakonsa don kaddamar da ita a matsayin 'yar fim. Hadiza ta fara fitowa ne a shekarar 2009, inda aka sanya ta a Artabu, ta samu shiga masana'antar fim ta kannywood a matsayin daya daga cikin manyan jarumai mata tare da taimakon Ali Nuhu da kuma jagorancin Aminu Shariff .
Takasance shahararriyar yar'wasan Hausa ce. Mutane da dama na gani da daukan ta amatsayin jarumar yar'wasan Kannywood kuma abar koyi musamman yadda take fitowa cikin sutura na al'ada da kyau. 



Hadiza takasance itace jakadiyanda ya daga cikin Camfani sadar na Nijeriya MTN Nigeria da kuma kamfanin abincin Indomie, ta karbi kyautar Best Actress Jury Award a 2nd Kannywood Award wanda kamfanin MTN Nigeria suka dauki nauyi bayarwa. Itace wacce ta kafa gidauniyar HAG Foundation