Bayan kutse da akayiwa jarumin mai suna Adam A. Zango tareda kwace masa shafinsa mai tarin mabiya kimanin miliyan daya da rabi a Instagram, wanda hakan ya. janyo rudani da kana nan maganganu a kannywood, tareda zarge zarge a tsakani, jarumin da kansa ya bayyana cewa baya isha shiga shafin nasa na instagram saboda kutse da akai masa, duk da cewa yana iyaka kokarinsa don shawo kan lamarin, amma idan abin bai yiwuba zai dangana ya bude sabon shafin, wanda kuwa hakan ne ya faru, a yanzu haka Adamu Zango ya bude sabon shafina mai laqabi da Sir_adam_a_zango, Amma ta bakin wani dan jarida mai suna Ahmad Naguda ya alaqanta kutsen da akayi ma shafin Adam A. Zango da taba 'yan luwadi da yayi a dan lokaci kadan da ya wuce wanda haka ya tunzura su sukayi masa wannann aika aika, Nagudu ya cigaba da cewa tunda yaga Adamu ya wallafa wa'azin Dr. Abdullahi Usman Gadon Kaya akan 'yan luwadi nasan cewa mutanen bazasu barshi, domin kungiya ce dasu mai karfi, tareda manya manyan mutane acikinta, Adam A. Zango ya godewa Allah ma da abin ya tsaya akan shafinsa na Instagram, ya kara dacewa lallai Adam A. Zango ya rinqa kiyaye wa da abinda zai wallafa koda ya kasance gaskiya ne domin yanzu duniyar ba akan doran gaskiya take tafiya ba. Jarumin ya dade yana nuna kyamarsa ga wannan harka ta luwadi wanda hakan ya jefashi rikici kala kala, Allah ya kiyaye mu baki daya ya datar da mu, Ameen.