API

History: Tarihin Abubakar S. Shehu - Directan Wakar SAMBISA

Tattaunawa ta Musamman da mai bada umarni kuma jarumi a kannywood Abubakar S. Shehu, Abubakar Darekta ne kuma jarumi, fina finan sa sun shahara matuka, tareda manyan wakokin da suka shahara a kafafen manhajojin zamani musamman Youtube wato Wakokin Sambisa wanda yamu baba da zainab sambisa suke hawa wanda mawaki liya-liya shike rubuta wakokin kuma ya rerasu mafiya yawancin lokaci.


An haifi Abubakar S. Shehu a garin jos, wanda a wannan gari na jos anan yayi makaranta da duk karatuttukansa kafin ya shiga harkar film, abubakar s.shehu ya fara samun ra'ayin film tun yana makarantar sakandari inda aka bashi shugaba na shashin wasan dandali na makaranta kuma shine yake shiryama makarantarsu duk wasan da za'ayi. bayan ya kammala makaranta alokacin yana sana'ar dinki sai ya fara harkar a matsayin jarumi inda yake fitowa a wasanni na gidan talabijin a garin na Jos.



Abubakar s. shehu ya bayyana irin wahala da yasha a harkar film inda ya sayar da duk wasu kadarorinsa domin ya shirya film, wanda bayan an kammala wannnan shiri kuma ankaishi kasuwa sai yazama asara amma duk da haka Abubakar bai gajiya ba ya cigaba da neman kudi kuma ya sake shirya wani film a karo nabiyu, wannan film da abubakar yayi a karo na biyu sunanshi shafin rayuwa, a wanann lokaci Allah ya taimaki Abubakar S. Shehu da samun nasara inda film din ya karmu kuma aka sami riba sosai, amma shi wannan shiri yayi sune duka a karkashin kamfaninsa na karan kansa mai suna E-sadiq Production, bayan wannan lokaci Abubakar S. Shehu darecktan wakokin sambisa ya hadu da abokansa guda biyu inda suka hada karfi suna kafa kamfanin 3sp International wanda shi 3 tana nufin mutum uku, S' tana nufin Stars sannan P' tana nufin Pictures wato 3 Stars Pictiures kenan, daga wannan lokaci Allah ya sanyama wannan kamfani nasu albarka inda mafiya yawancin finafinan kamfanin suna samun tasiri da karbuwa.

Abubakar S. Shehu ya sami ilimin harkar film daga manyan mutane musamman masu gidanshi dake garin Jos irinsu Auwalu Salihu, Waziri Zayyanu da kuma Sani Mu'azu Gwamna a shirin arewa24 na kwana casa'in.

a Karshe darektan yabama matasa da abokan harkarsa na Kannywood shawara da su tashi tsaye wajen neman ilimi na harkar film da bincike don inganta harkokinsu da samun cigaba.