Malamin nan mai abin mamaki wanda labarinsa ya ja hankali da dama wanda ya bayyana ya auri aljana kuma har suna da yara da ita, batunda ya dauki hankalin kafafen labarai na duniya da dama, a wannan karo Muryar Amurka bangaren hausa ne suka ziyarceshi da azumi inda suka bukaci a kawo musu girkin aljana kamar yanda ya bayyanama duniya cewa aljanar tana yi masa kirki ta kawo masa, saida Malam Ahmad Ali Kofar na'isa ya bayyana musu cewa basu sa'ar zuwa ba saboda yau ba ranar girkin ta bane amma bayan Ramadan su zo zasu ci abinci na girkin Aljana da yardar Allah.
Abin mamaki duk da hakurin da ya basu bai barsu haka ba sai da wasu abubuwan mamaki suka auku a wannan waje inda a gabansu aljanar ta kawo masa kudi sababbi dubu dubu da sarka harda alhariri na kayan Sallah, abinda ya bar jama'a da dama cikin mamaki tareda sanya waswasi a zukatan masu karyata malamin a farko.
A kwanakin bayane Malamin ya bayyana yanda ya hadu da aljanu inda yace hakan ya auku ne tun yana karamin yaro alokacinda ya hwada rijiya shida mahaifiyasa aka sami mahaifiyarsa shikuma aljanu suka tafi dashi wajensu inda yayi rayuwarsa a can kusan shekara shida kafin suka dawo dashi wajen mahaifiyarsa kuma sarkin aljanu ya bashi 'yarsa har ya aure, malamin ya bayyana cewa aljanar tana daukarsa su tafi yawon duniya kamar su saudiya, birnin sin harma da inda mutane basa zuwa kuma har daukar hotuna yake a can.