duk da radadi da azaba dake cikin zana suna a jikin fata amma duk da haka saurayin ya daure ya zana sunan matashiyar jarumar wato Ummi rahab a jikin hannunsa.
Ita dai ummi rahab ta fara shirin hausa tun tana yar kankanuwa kuma yanzu da ta dan taso ta fara fitowa a fina finan kuma tauraronta na haskawa matuka.
Ummi rahab ta kasance yar bangaren Adam A. Zango inda a Ya sanyata a shirinsa mai dogon zango na Youtube wato shirin farinwata sha kallo, inda wannan shiri shine ya zamanto mata bakandamiyar shiri tunda ta dan data.
Soyayyar da wannan saurayi ya nunawa ummi rahab yanada alaka da irin haskawa da jarumar take musamman videos nata na tiktok da suka karade kafafen sada zumunta da dama, kuma jarumar ta kasance mai karamin shekaru, farace kuma kyakykyawa.