API

PENSIONERS PRAISE PRESIDENT BUHARI FOR PAYING THEIR PENSIONS WITH ARIYAS

ƳAN FANSHO SUN YABA WA SHUGABA BUHARI BISA BIYAN SU KUƊAƊEN FANSHO DA ARIYAS 



Fassara: Hon. Buhari Sallau Hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari Bangaren Rediyo da Talabijin.


Ƴan fansho a Najeriya karkashin Ƙungiyar Ƴan Fansho na Ƙasa, (Nigeria Union of Pensioners) sun rubuta wasikar Godiya da Jinjina ga Shugaba Muhammadu Buhari, kan biyan kaso Mafi tsoƙa na kuɗaɗen hakkin su da suke bin a baya. 


Cikin wasikar wanda ke dauke da rattaba hannun Babban Magatakardan Ƙungiyar, Elder Actor Zal. Ƴan fanshon sun bayyana Buhari a Matsayin Shugaba "wanda ke sauraron da Nuna So da ƙyakƙyawar fata" ga wannan batun" ya nunar cewa hakan shaida ce ta "kokari da Gwamnatin sa tayi domin sanya fuskokin mebobin mu cikin annashuwa."


Ga abinda wasikar ta ƙunsa nan biye:


"Shugabanni da duk daukacin membobin na Kungiyar Fansho, suna fatan bayyana farin ciki ga Mai girma Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari GCFR, dangane da bada iznin biyan hakkin Ƴan Fansho da samar da kuɗaɗen domin biyan cikin ƙanƙanin lokaci na kuɗaɗen ariyas na shekaru biyu. 


"Duk da kalubalen da tattalin arziki ke ciki, daga lokacin da aka saki takardan iznin, Shugaban Kasa ta hanun Hukumar shirya biyan kuɗaɗen fensho suka fara biyan Ƴan Fansho da duk daukacin ƙasa, ta Gurin fara biyan na watanni Goma sha biyu, 12 wanda tuni aka fara a watan Shida, da kuma sake biyan watanni Shidda a cikin watan Bakwai, wanda ya rage watanni shida kawai ya rage. Muna fatan cewa za'a ka rasa biyan a lokacin daya dace. 


"Ƙungiyar ta lura da irin gagarumin kokari da nuna damuwa da Gwamnatin ka tayi don sanya annashuwa a fuskokin membobin mu dake Ƙasa baki daya, ya zamo wajibi mu nuna godiya wa Gwamnatin ka. 


"Wannan aikin da kayi kawai yana kara shaida gaskiyar cewa kai, babu shakka shugaba ne mai sauraron wanda ke bukatu. 


"bamu da bakin maka Godiya 


Femi Adesina:

Mashawar ci Na Musamman ga Shugaban Kasa a Fannin Yada Labaru da Wayar da kan Jama'a.

03 ga watan Ogusta , 2021