API

Igbo and Hausa Marriage - Aure Tsakanin Igbo da Hausa

Shin inyamuri zai iya bada 'yarsa ga bahaushe ko kuma bahaushe ya auri inyamura?

Wannan tambaya tana damun mutane da dama hausawa da inyamurai duka, saboda irin banbancin tsarin rayuwa da addini dake tsakanin bahaushe da inyamuri, tareda rashin yarda musamman ta siyasa da tayi tsamari a tsakanin taren guda biyu. 
kafin mu amsa wannan tambaya akwai bukatar muyi waiwaye kan tarihin siyasar najeria tun samun 'yanci. 

aure



lokacinda aka baiwa najeria 'yanci a shekara ta 1960 bahaushe ya kulla alakar siyasa mai karfi tsakaninsa da inyamiri inda Aka baiwa Sir, Alhaji abubakar tafawa balewa prime minister na najeria shikuma Sir Azikwe wanda yake inyamiri ne aka bashi shine president a wannan lokaci, sunyi mulki cikin amana da soyayya da juna tareda hadin kan kasa sosai duk da banbanci mai karfi dake tsakaninsu na addini, amma suka hada kai don cikagaban kasar Najeriya. 

ana cikin haka kwatsam sai wasu group na sojojin inyamurai sukayi juyin mulki inda suka kashe kusan duk wani babban shugaba na arewa Hausa-fulani, daga cikin manyan wadanda aka kashe akai shuga premiere na arewa wato Sardauna, dakuma shugaba tafawa balewa tareda manyan shuwagabanni na yarabawa.

kashe wadannan manyan shuwaganni da hausawa ke ji dasu yayi ma duk wani bahaure dan arewa zafi har rana mai kama ta yau, wanda hakan yasa sojojin arewa suka dau fansa tareda kara yin juyin mulki.

tun daga wannan lokaci rashin yarda tsakanin inyamuri da bahaushe ya shiga amma duk da haka tsirarun hausawa suna auran yaran mata inyamurai amma abu ne mai wahala bahaushe yaba inyamuri 'yarsa.


SHIN BAHAUSHE ZAI IYA BAYARDA 'YARSA GA INYAMURI?
Wannan tambaya alal hakika tana da nauyi amma mafi akasarin lokaci hausawa basa bama inyamuri 'yarsu sai dai in musulmi ne ko ya yarda ya musulunta, ko kuma dukaninsu sun tayuwa ne a wata kasa da suke da doka da tsari na 'yancin dan adam kamar amurka , birtaniya da sauransu. amma abune mai wahala bahaushe ya bama inyamuri 'yarsa da aure.

SHIN BAHAUSHE NA AURAR INYAMURA? 
sosai kuwa hausawa da dama sun auri mata inyamurai saboda kyaunsu, iya rike miji da iya jiyar da miji dadin aure, amma mafiya yawan wadanda suke auran mata inyamura zaka samu attajirai ne,  ko ‘yan siyasa ko sojoji.