Nafisat Abdullahi wacce aka fi sani da Nafisa sai watarana ta dakatar da kanta a shirin film Mai dogon zango mai suna Labarina wanda ake haskashi a tashar Arewa24.
Ga dai cikakken bayanin da ta wallafah :
👇👇👇👇
PUBLIC ANNOUNCEMENT!!!
Labarina Project ne da nake alfahari da shi ah duk inda na shiga. Saira Movies is also like my own company because mun Jima Muna aiki tare. I’m very sad to let you all know bazan ci gaba da Aikin Labarina ba, dalili shine rashin samun lokaci na yadda ya kamata, i have my own businesses, school, a company to run and also my own films that I’m planning to start shooting very soon. Bazan ce ah jira ni sai sanda na samu lokaci ba, dole za’a ci gaba da film din Labarina ko da ni ko ba ni.
Ina ba dubban masoya hakuri Akan fita ta daga shirin. Alakata da Saira movies Zata ci gaba da tafiya lafiya, babu hayaniya ko cin zarafi, Allah Kuma ya basu sa’a Wajen kammala sauran shirin.
— Nafisat Abdullahi.
Ga Cikakken Labaran a faifan Bidiyo 👇👇👇