Ikon Allah : Yadda Bayo Ya Zama Mai Daukan Hoton Buhari Ba Tare Da Yasan Kowa Ba

Abin mamaki ne matuka yadda bayo dan talaka da bashi da hanya a sama ko kadan ya zama babban mai daukan hoton shugaban kasa a zamanin shugaba Muhammadu buhari.





Abin mamaki ne ganin yadda Bayo Omoboriowo, mai daukar hoto na Buhari ya bayyana a hira a gidan talabijin na Channels TV 

Sun tambayashe : Yaya aka yi ka zama mai daukan hoton Buhari a hukumance? 


Bayo: Ina gaya muku, labari ne daga Mushin har duniya. Mahaifina mai daukar hoto ne na gida. Na tuna nima na yi yawon sayar da ruwan pure water. 


Mahaifina ma bai san shugaban karamar hukumar mu ba balle ya yi maganar wani babban dan siyasa. 


Na je Jami’ar Legas na yi karatun Chemistry wato ilimin sinadarai, Na gama da maki ma sakamakon 4.262 GPA. 


Yayin da nake makaranta, na ari kyamara daga abokina kuma na fara ɗaukar hotuna daban daban, musamman abubuwan da suke faruwa alokacin.


Watarana ina kallon Talabijin sai na ga an tallata taron jam’iyyar APC na kasa a filin wasa na Teslim Balogun. 


Sai na ɗauki kyamarata na tafi, Lokacin da “Janar Buhari” ya shigo filin wasa sai kowa ya fara binsa da gudu, ni kuma na bi shi ina daukar hotuna. 


Sai na lura sun saci wayar iphone dina, wayar sama da N100,000 a lokacin. Na yi bakincikin abinda ya faru da ni na sace min waya kuma na ji zafi. 


Don haka na ce wa Allah, na roki Allah kuma na kai kuka na ga Allah cewa Allah ya mayar min da wani abubu mafifici, ban taba sanin Allah ya ji. 


Don haka ba zan iya komawa gida a daren ba, na kwana a kasa a cikin filin wasa. 


Ban taba sanin wasu sun gan ni ba. Daga nan aka fara yakin neman zabe. An tuntubi wani kamfanin yada labarai don gudanar da yakin neman zaben shugaban kasa na kafofin sada zumunta. 


Kamfanin ya lura ba za su iya yin aiki da kyau ba tare da Mai daukar hoto ba. Saboda haka,  daya daga cikinsu ya ganni ina barci a kasa a wancan  lokaci, an tuntube ni. 


Mun fara aikin yakin neman zabe a haka Janar Buhari ya dauke ni. 


Bayan Zabe, sai ya aika a kira ni, kuma ya ce ya lallai ni din nan hake so nazo na rinka daukar hotunan shi. 


Ta haka ne na zama mai daukar hoto a hukumance na tsawon shekaru 8 kuma duk inda shugaba Buhari zai je a duniya da ni yake zuwa.


Na kuma sami lambar yabo ta gida da waje da yawa sakamakon aiki na da shugaban kasa.