Fatima Hussain : Wani Mutum Ya Saya Wa Jarumar Labarina Maryam Mota

Wani Bawan Allah Ya Saya Wa Jarumar Maryam Ta Shirin Labarina Mota.




Wani bawan Allah mai kallon shirin Labarina ya gwangwaje Fatima Hussain (Maryam Labarina) da Kyautar sabuwar Mota kirar Honda ta zamani.


Motar da aka sayawa jaruma Maryam ta labarina


Mutumin ya bayyana dalilin kyaurar motar inda yake cewa yayi mata kyauta motar ne saboda birgeshi da tayi na nuna halin gujewa duniya da gudun son abin duniya da ta nuna a shirin labarina, wanda hakan yayi matukar birgeshi.

Tuni dai jama’a da dama sukai ta tofa albarkacin bakinsu musamman a kafafen sada zumunta, inda wasu suke mata fatan alheri da yaba masa da irin wannan hida, a daya bangaren kuma wasu ke nuna zargi da rashin aminta da kyautar.





Jaruma Fatima Hussain dai ‘yar asalin Kaduna ce, wacce tauraron ta ya fara haskawa a sabon shirin labarina na Aminu saira, labarin ya dauki hankalin jama’a da dama lura da dimbin darasin da shirin ya kunsa.


Aminu Saira


Hazikin darektan nan mai basira da akafi sani da Aminu Saira shine wanda ya bada umurnin shirin, shirin kuma yana da babban jarumin Hausa Sadik Sani Sadik wanda ya  fito a matsayin mai nasara.