Manjo Janar Danjuma Ya Zargi Hanun 'Yan Ta'ada A Kisan Tsohon Shugaban Sojin Najeriya, Janar Attahiru

 INA GANIN DA HANNUN MASU DAUKAR NAUYIN TA'ADDANCI A MUTUWAR JANAR ATTAHIRU-MANJO JANAR KEFFI MAI RITAYA


Tsohon kwamandan rundunar soja a Kaduna Manjo Janar Danjuma Ali Keffi mai ritaya ya nuna kokonto yanda a ka yi hatsarin jirgin saman da ya yi sanadiyyar mutuwar tsohon babban hafsan sojan kasa Janar Ibrahim Attahiru.




In za a tuna a 2021 Janar Attahiru da tawagar sa sun rasa ran su a hatsarin jirgin sama a daf da filin saukar jiragen sama na Kaduna.

Ali Keffi a labarin da jaridar yanar gzio ta Premium Times ta wallafa, ya zargi yiwuwar makarkashiyar kashe Attahiru kan masu daukar nauyin 'yan ta'adda da ke ciki da wajen rundunar sojan Najeriya.

A bayanan Manjo Janar Danjuma Keffi wanda ya ce an daure shi da yi ma sa ritayar dole; akwai tambayoyi da yawa kan yanda jirgin da ke dauke da Attahiru ya yi hatsari.




Wasu dalilan da Keffi ya bayar akwai jinkirta lokacin tashin jirgin daga Abuja, tashin jirgin daidai lokacin da gagarumin hadari ya taso a Kaduna, saukar jirgin a filin jirgin saman farar hula maimakon na soja da sauarn su.

Hakanan Keffi ya ce a daidai inda jirgin ya fadi ba a samu tonon wani rami ba kamar yanda in jirgi kenan ya fadi, wanda ke nuna jirgin ya riga ya tarwatse tun daga sama kafin sulmuyowa kasa.

Kazalika Keffi ya ce sun tsinci gawawwakin marogayan a gefe can da inda jirgin ya ke kuma an same su a babbake.

Ba mamaki abun da ya fi ba wa Keffi takaici shi ne yanda bayan daure shi ko tsare shi da a ka yi na kimanin kwana 60 tsohon shugaba Buhari bai yi yunkurin ceto shi ba.

Keffi ya bukaci shugaba Bola Tinubu ya duba kadun abun da ya same shi da binciko fayel din yanda jirgin attahiru ya yi hatsari.