SHUGABA TINUBU YA AMINCE DA SAMAR DA NA'URORIN TSARO A ABUJA - WIKE

Ministan babban birnin taraiya Abuja Nyesom Wike ya baiyana cewa shugaba Tinubu ya ba da amincewar gaggawa don odar na'urorin tsaro.


Tinubu and Wike


Wike na magana ne a taron ganawa da manema labaru na farko da ya gudanar a sabuwar shekarar nan ta 2024.

Wike ya ce shugaba Tinubu ya amince ba da wani jinkiri ba a samar da na'urorin don taimakawa aiyukan jami'an tsaro wajen yaki da masu satar mutane da sauran miyagun iri.


Ministan ya ce da zarar an kafa na'urorin za a iya ganin miyagun irin da kuma yanda jami'an tsaro za su bi sawun su inda inda su ka makale a birnin.


Hakika wasu mazauna Abuja musamman amsu hannu da shuni na nuna fargaba kan yiwuwar sace su inda akasari talakawa ke gudanar da harkokin su kamar ba labarin komai na tabarbarewar tsaro.