Jihohi mafi yawan al'umma a Najeriya na taka muhimmiyar rawa wajen tsara yanayin zamantakewa da tattalin arzikin kasar, wanda ke nuna bambancin al'adu, karfin tattalin arziki, da kuma muhimmancin tarihi.
Najeriya ita ce kasa mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka, tana da tarin al'adu da karfin tattalin arziki mafi girma a duk Afrika.
Arzikin wannan kasa ya samo asali ne bisa jumullar illahirin karfin arzikin jihohin da ke cikinta da yawan jama’ar su, Najeriyariya na da jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja da ke arewa maso tsakiyar kasar.
Daga cikin wadannan jihohi 36, akwai 7 mafiya yawan jama’a da karfin tattalin arziki, kowannensu yana bayar da gudunmawa sosai ga yanayin zamantakewa da tattalin arzikin Najeriya.
1. Jihar Legas:
Legas, wanda kuma aka fi sani da birnin Legas, shi ne birni mafi girma a Najeriya, inda mutane kusan miliyan 21 ke zaune acikin sa. Ba wai birni mafi girma a Najeriya kadai ba, har ma da yankin da ya fi cunkoso a Afirka.
Legas ne babban birnin tarayyar Najeriya tun zamanin turawan mulkin mallaka kafin ya koma Abuja a zamanin soji na Janar Ibrahim Badamasi Babangida a shekara ta 1991.
Legas muhimmiyar cibiyar hada-hadar kudi ce, wacce ta shafi kasuwanci, nishadantarwa, fasaha, da sauransu a fadin Afirka. Yana daga cikin biranen da suka fi saurin bunkasuwa a duniya kuma yana da karfin tattalin arziki, a matsayi na hudu a Afirka. A kwai tashar jirgin ruwa dake hade da tekun atlantica da ya hade da duniya wanda hakan na daga cikin manyan hanyoyin kudin shiga na jihar.
Alkaluman yawan jama'a na Babban Birnin Legas sun bambanta, tare da kiyasin daga miliyan 16 zuwa kusan miliyan 21 a shekarar 2015.
2. Jihar Kano:
Kano Jiha ce a Najeriya da ke yankin arewacin kasar. Ita ce jiha mafi yawan jama'a a Najeriya, bisa ga kidayar jama'a ta 2006 da kuma kididdigar 2016 da Hukumar Kididdiga ta Kasa ta yi. An kafa ta a shekarar 1967 daga tsohuwar yankin Arewa, jihar Kano tana da iyaka da jihar Katsina, da jihar Jigawa, da jihar Bauchi, da kuma jihar Kaduna. Babban birninta kuma mafi girma shine Kano, birni mafi yawan jama'a a Najeriya.
A tarihance, Jihar Kano ta kasance wurin masarautu daban-daban, ciki har da Masarautar Kano. Yankin ya kasance cibiyar hada-hadar kasuwanci tun karni na 15, inda Kasuwar Kurmi ke taka rawar gani.
Jihar Kano jiha ce da ke da rinjayen musulmi da tarihin musulunci, mafiya yawan al’ummarta sun ƙunshi kabilar Hausa-Fulani, waɗanda ke ba da gudummawa wajen kiyaye al’adun da addini.
Harkokin al’ummar wannan jiha shine Noma, kasuwanci, da harkokin masana'antu wanda ke samar da ci gaba a cikin jihar da ma wajenta. kuma yawan jama’ar jihar ya kai akalla miliyan 16.
3. Jihar Katsina:
A matsayinta na daya daga cikin manyan jahohin Najeriya a fadin kasa, Katsina na da matukar muhimmanci saboda yawan al'umma da noma. Jihar Katsina tana arewa maso yammacin kasar kuma kabilar Hausa-Fulani ne mafi yawan mazaunanta, wadanda suke sana’ar noma da kiwo. Jihar na da yawan al’umma kimanin miliyan 11
4. Jihar Kaduna:
Jihar Kaduna na yankin kusa da tsakiyar Najeriya, ta yi fice a matsayin matattarar kabilu daban-dadan dake arewacin Najeriya duk da cewa kabilar Hausa Fulani sune mafiya rinjaye kuma a jihar ne babbar masarautar Zazzau take. Tun asali jihar ita ce cibiyar gudanarwar sojoji a lokacin mulkin mallaka. Bugu da kari, jihar Kaduna itace shalkwatar Arewacin Najeriya a lokacin mulkin yanki.
Ta fannin tattalin arziki jihar Kaduna na bunkasa a fannin noma, hakar ma'adinai, masana'antu, da ayyuka. Bangaren masana'antu kuma sun hada da masaku da masana'antar sarrafa abinci, sutura da dai sauransu.
Ilimi yana taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban Jihar Kaduna, inda cibiyoyi irin su Jami’ar Ahmadu Bello da Jami’ar Jihar Kaduna ke ba da gudunmawa wajen bunkasar ilimi haka kuma makarantar horar da sojoji wato NDA a jihar Kaduna take.
Jihar na da yawan al’umma kimanin miliyan 9
5. Jihar Oyo:
Jihar Oyo, dake kudu maso yammacin Najeriya, tana da tarihi mai cike da al'adu kuma jiha ce ta kabilar Yarabawa.
A tarihi, Oyo ta kasance muhimmiyar cibiyar daular Oyo, daya daga cikin manyan jihohin Yarbawa mafi girma da karfi a Najeriya kafin mulkin mallaka. Masarautar ta bunƙasa tun daga ƙarni na 14 zuwa na 19. Ta shahara saboda bajintar soji, da karfin ikonta a yankin Yarabawa, jihar na da yawan al’umma kimanin miliyan 8
6. Jihar Ribas:
Jihar Rivers, dake yankin Neja Delta, ta kasance cibiyar tattalin arziki da al'adu a Najeriya. Jihar na dauke da al'ummai daban-daban da suka ƙunshi ƙabilu na asali kamar kabilar Ijaw, Ikwerre, da Ogoni. Tattalin arzikin jihar ya ta'allaka ne kan aikin hakar mai da iskar gas, ayyukan teku, da kasuwanci, wanda ke ba da gudummawa sosai ga kudaden shiga na kasa.
Jihar Ribas na da yawan jama’a da ya kai akalla 7.4
7. Jihar Ogun:
Da ke kudu maso yammacin Najeriya, jihar Ogun ta yi suna saboda bajintar masana’antu, yawan noma, da kuma tarihi. Tare da yawan al'ummar Yarbawa mafi rinjaye, Ogun tana da kyawawan al'adun gargajiya, wanda ke bayyana a cikin bukukuwanta, al'adun gargajiya.
Kusancin da jihar ke da shi da Legas ya taimaka mata wajen bunkasar tattalin arziki da samun masu zuba hanun jari. Yawan al’ummar jiyar ya kai kimanin miliyan 6.3