Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da rushe illahirin masarautun jihar Kano wadanda aka kirkira a lokacin gwamnatin baya ta Abdullahi Umar Ganduje, hakan ya biyo bayan soke sabuwar dokar da ta kirkiri sababbin masarautu a shekarar 2019.
Majalisar ta dauki wannan mataki ne biyo bayan muhawara da aka tafka a zauren Majalisar a ranar Alhamis, 22 ga watan Mayun 2024
shi dai Wannan mataki ya zo ne bayan da Majalisar ta sake nazari tare da zartar da dokar alokacin da suka kai tsallake karatu na biyu da na uku.
Shi dai wannan batun rarrabuwar masarautu ya samo asali ne tun lokacin da gwamnatin baya ta Abdullahi Umar Ganduje ta tsige Sarki Muhammadu Sunusi II, inda ta bayyana dalilanta da suka hada da zarge-zargen almundahana da zargin rashin da'a.
Muhammad Bello Butu-Butu shi ne Mataimakin Shugaban Majalisar wanda ya bayyana batun da dalilan da suka janyo rushe masarautun.
Butu-Butu ya bayyana cewar “soke dokar data rarraba masarautun Kano zuwa gida 5 zai taimaka wajen dawo da martaba Kano data zube". inji Batutu
bugu da kari, ya kara da cewar, "raba masarautar Kano zuwa gida 5 ya rage kima da martabar jihar."
Shima Shugaban Masu Rinjaye a majalisar, Lawan Husseini Dala, ya bayyana illar rarraba masarautun ga al'adun Kano.
inda ya bayyana cewa, "masarautar ta kasance wata ma'ajiyar tarihi da al'adun Kano, wacce aka lalata sakamakon kirkirar karin masarautu.
Yayi karin hasken cewar, manufar gyaran dokar itace dawo da martaba da hadin kan da aka san masarautar Kano dasu.” inji Husseini Dala
Masarautun da aka rushe dai sun hada da masarautar Kano da ta Bichi da ta Karaye da ta Gaya da kuma ta Rano.
Dokar ta yi tanade tande guda 51, hakan ya biyo baya ne kamar yadda majalisar jihar ta Kano ta bayyana a lokacin da ta yi wa dokar gyara a shekara ta 2019.
Ga wasu muhimmai daga cikin su.
- Gwamna ne zai zabi shugaban majalisar sarakuna da za a kafa nan gaba
- Gwamna ne zai nada masu zabar sarki a duk lokacin da bukatar hakan ta taso
- Duk sarkin da gwamna ya zaba don shugabantar majalisar sarakuna, zai jagoran ce ta ne tsawon shekaru biyu
- Duk sarkin da ya ki halartar tarukan majalisar sarakunan har sau uku ba tare da kwakkwaran dalili ba, ya kori kansa daga sarauta.