Sojoji da manyan masu fada aji na Najeriya sun dade suna kira ga hukumomin binciken sirri na kasar da su bibiyi masu ɗaukar nauyin ta'addanci a Najeriya.
Matsalar tsaro na cikin manyan batutuwa da kalubale da suka haddabi kasar Najeriya, musamman arewacin kasar. Umar Dikko Radda shine gwamnan katsina da ke arewa maso yammacin kasar, jihar Katsina na daga cikin manyan jihohin arewa da ke fama da matsalar tsaro na 'yan ta'adda da 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa.
A wani faifan bidiyo da ke yawo a internet, Radda yayi bayanin irin fadi da girma da harkar tsaro take a Najeriya, inda ya bayyana cewa bai fahimci girman al'amarin ba sai da yazama Gwmana. Bugu da kari, gwamnan ya bayyana cewa lallai sunyi bakin jini sosai sakamakon rashin amincewa da sulhu da yan ta'adda, musamman shi da gwamnan zamfara.
"Bashi yiwuwa kayi sulhu da dan ta'adda alokacin da kaine mai rauni" inji Gwamna Umar Dikko Radda.
Har ilayau gwamnan ya bayyana cewa irin mutanen da ke cikin wannan harka ta tabarbarewar tsaro suna da matukar yawa kuma sun wuce duk tunanin mutum, wanda baka tunani zai shiga irin wannan harka sai kaga har da shi a cikin ta.