API

Yadda Akayi Bikin Rantsar Da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II A Karo Na Biyu

An guda nar da bikin ne a gidan gwamnatin jihar kano a ranar juma'a 24 ga watan Mayun 2024.Biyo bayan sanarwar dawo da sarkin daga mukaminsa wanda alokacin gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje yayi na tsige sarkin daga mukaminsa a shekara 2019.


Abba Kabir Yusuf, Gwamnan Kano mai ci ya rattaba hanu kano dokar dawo da sarkin bayan muhawara a majalisar jaha, wacce ta samar da garambawul ga dokar masarautar jihar tare da rushe dukkan masarautun da aka kirkira a lokacin ganduje.


Kalli Yanda Akayi Bikin Rantsar Da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II


Jagoran jam'iyyar NNPP a Najeriya kuma tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana ra'ayinsa kan dawo da Sarki Muhammadu Sanusi na biyu kan karagar mulki da aka yi, inda a wata hirar sa da BBC Hausa, ya bayyana cewa bashi da hanu kan wannan batu amma zai je kano ya sami gwamna don samun bayani game da lamarin.