API

Rikici Tsakanin Hadiza Gabon Da Zaharaddeen Kan Hana Mata Shiga Kannywood

Zaharaddeen Sani ya chachchashe Hadiza Gabon kan maganar da tayi na bada shawara ga mata masu son shiga harkar film kan cewa kada su shigo. A Sabon rikici ya barke tsakanin jarimi Zaharaddeen Sani da Hadiza Aliyu Gabon akan maganar da  tayi a shirin ta inda take baiwa mata shawara kan cewa kada su shigo film wato kannywood.

Jarumar ta bayyana haka ne a shirinta na Gabon Showroom inda take hira da Jarumar matashiya wato Rayya Kwanan Chasa'in na Arewa24. Jarumin da yake yi mata martani, ya bayyana rashin jin dadinsa kan kalaman jarumar akan film, inda ya bayyana cewa duk wata daukaka da jarumar ta samu a yanzu ta dalilin film ne, don haka babu yadda za'ayi ta kushe masana'antar.



Wannan shine cikakken bidiyon rahoton

Bugu da kari, Zaharaddeen ya bayyana cewa duk wani zagi da ake yiwa 'yan fim mafi yawanci irin su Hadiza Gabon din ne ke janyo wa da yake bayyana zargin nasa. Har ilayau jarumin, ya bayyana cewa ko 'yarsa tace masa tana son film baby shakka zai barta ta shiga saboda su sun dauki abin a matsayin sana'a ne.