Farfesan ya bayyana cewa rikicin ba akan Sarki Muhammadu Sanusi II aka fara ba kuma hasalima tun bayan rikicin Muhammadu Sanusi na daya da Sardauna wanda yayi sanadiyar tsige shi daga mukamin sarkin kano, za'a iya cewa abinda ya kawo Ado Bayero kan mulki shima rikicin ne, saboda Ado Bayero na can gefe aka dauko shi yayi sarauta saboda da rikcin da ke da alaka da siyasa.
Haka zalika, Ado Bayero da kanshi ya fuskanci matsaloli da barazanar tsigewa daga tsohon gwamna Abubakar Rimi wanda hakan nada alaka da siyasa kamar yadda ya faru na dalilin kawo Sanusi Lamido Sanusi da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso yayi da kuma yadda ta kaya da Gwamna Ganduje da Muhammadu Sanusi II wanda yayi sanadiyyar kirkiran sabbin masarautu da zuwan sarki Aminu Ado Bayero zuwa yau da gwaman Abba Kabir Yusuf ya tsige shi ya dawo da Muhammadu Sanusi II.