Matashiyar mai suna Zainab ta ce "an haife ni da Baiwar zane-zane da kayan Marmari kuma babu wanda ya koya min"
Matashiyar mai suna Zainab Shu’aibu Zakari ta bayyanawa Muryar Amurka yadda ta gano tana da baiwar zane-zane na sassaka da kayan marmari.
(Bidiyon yadda matashiyar ta nuna baiwar ta na zane zane da kayan marmari)
Zainab tace babu wanda ya koya mata, duk abinda take baiwane daga Allah, inda take zuwa kasuwar lemo da ke kano ta sayo kankana ta zo gida ta fara sarrafa izuwa abubuwa daban daban ta hanyar sassaka da zane-zane.
Har ilayau Zainab tace tana da burin ganin ta koyar wa wadan su musamman matasa mata irinta ta yan zasu dauke shi a matsayin sana’a ta dogaro da kai.
Babu shakka irin wadan nan labarai sun zama wasu abubuwa da ke karfafa ma masu baiwa irin ta Zainab a fannoni daban daban wajen tashi su baiyana hazakar su da amfani da baiwarsu wajen samar wa kai aikin yi da sana’a, harma da koyarwa wasu don su amfana da amfanar al’umma.