Attajirin da ya fi kowa kudi a Najeriya, kuma shugaban rukunin Dangote, Aliko Dangote, ya tattauna batutuwa daban-daban a kwanakin baya, da suka hada da bude katafaren matatar mai da ya ke yi, da batun cire tallafin man fetur da gwamnati ke yi, da kuma samar da man fetur a kasar. A wata fira da ya yi da Bloomberg, Dangote ya yi karin haske kan kalubale da damammakin da matatar ta sa ke kawowa ga tattalin arzikin Najeriya da yanayin makamashinta.
Matatar Dangote za ta zama mai kawo sauyi ga bangaren makamashin Najeriya, da share fagen samun daidaiton tattalin arziki, da rage shigo da mai, da sarrafa albarkatun man kasar. Kokarin da Dangote ya yi ba wai ya nuna wani muhimmin ci gaba ba ne kawai, har ma yana nuna wani sabon zamani ga Najeriya a harkar mai a duniya.