API

Jawabin Shugaba Tinubu Da Hausa Na Ranar Bikin Samun 'Yancin Kan Nijeriya Karo Na 64

Shugaba Bola Tinubu ya yi jawabi ga al’ummar Najeriya ne a inda ya yaba da irin gwagwarmayar da ‘yan Najeriya da dama suka fuskanta tare da bayyana irin kokarin da gwamnatinsa ke yi na shawo kan wadannan kalubale ta hanyar kawo sauyi mai dorewa.

Shugaba Tinubu yace yana sane da irin halin tsadar rayuwa da illahirin al'ummar kasar ke ciki, ya kuma tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa yana jin muryoyinsu, kuma gwamnatinsa ta dukufa wajen lalubo hanyoyin da za a bi domin rage musu radadin da suke ciki. 

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da hakuri, yana mai cewa sauye-sauyen da ake ci gaba da samu sun fara bayyana kuma alheri na nan zuwa nan gaba kadan ba da jimawa ba.


Ga cikakken rahoton na bidiyo a kasa :



Wannan shine cikakken rahoton jawabin shugaban na Najeriya Bola Ahmed Tinubu a ranar bikin samun 'yancin Najeriya na 1 ga watan Octoba.