API

Sheikh Alkali Abubakar Salihu Zaria Yace: Kudin Kirifto Halal Ne

Shehin Malamin ya ambaci haka ne a wata hira ta musamman da muryar Amurka, inda dan jaridar yayi masa tambayoyi game da maganar sa akan kirifto da ta bar baya da kura da kuma korafe korafen malamai akan sa game da salon wa'azinsa da ke kama da barkwanci.

Ga cikakken rahoton na bidiyo a kasa:

Najeriya tana kan gaba a cikin jerin kasashen duniya da suka rungumi sauyin canjin kudin dijital wato Kudin kirifto. A bisa binciken shafin coinpeedia.org yace sama da mutane miliyan 22 ne a Najeriya ke hada hadar kudin kirifto wato kaso 10.3% na al’ummar kasar.

Duk da irin wadannan nasarori, kudin na kirifto na fuskantar manyan kalubale da suka hada da haramcin hada hadar sa tsakanin bankunan kasar wanda babban bankin Najeriya na CBN ya shar’anta.