A kasar da miliyoyin mutane ke dogaro da motocin da ke amfani da man fetur wajen gudanar da harkokinsu na yau da kullum, ‘Yan Najeriya sun shiga wani mawuyacin hali. Farashin man fetur yayi tashin gwauron zabi, ya ninka fiye da ninki hudu, daga Naira 195 izuwa 1030 A Abuja harma fiye da haka a wasu sassan kasar.
A watan Mayun 2023, gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yanke shawarar cire tallafin mai, wanda ya haifar da hauhawar farashin man fetur din. Gwamnatin tace matakin na da nufin daidaita tattalin arzikin kasar, kuma a karshe al’ummar kasar zasu dara cikin farin ciki.
Irin wannan tsaka mai wuya da ‘yan kasar suka tsinci kansu aci, Har yanzu ana cigaba da jin tsananin matsin tasirin cire tallafin na Man fetur a fadin kasar, tun daga garin Legas zuwa Birnin Abuja da sauran illahirin garuruwan Najeriya.
Babbar Tambayar Anan Itace, Yaushe wannan wahala zata Kare?
Kuma mene ne Mafita?
A wani gagarumin yunkuri na rage dogaron da Najeriya ke yi kan albarkatun man fetur, gwamnatin Najeriya ta fito da wani shiri na sauya sinadarin sufuri na ababen hawa daga man fetur izuwa amfani da iskar Gas samfurin (CNG).
Haka Zalika, Gwamnatin ta bada sanarwar dakatar da harajin VAT kan Iskar Gas da dukkanin danginsa, wanda hakan na nufin nuna kokarin samar da farashi mai rahusa da mafita ga sayan man fetur mai dan karan tsada.
Canza mota daga man fetur zuwa CNG ya ƙunshi gyare-gyare da yawa ga injinta da tsarin man fetur. Na farko, ana shigar da Na’urar CNG ɗin a cikin motar, wanda ya haɗa da abubuwa kamar babban tanki mai ƙarfi, layin sarrafa mai da dai sauran su. Haka zalika, akwai aikin daidaita sigogi kamar lokacin kunna wuta da ƙimar iskar mai don haɓaka aiki da inganci.
Duk da fa’idojin da ke tattare da sauya motoci izuwa amfani da iskar gas samfurin CNG, wanda ya hada da rashin tsadar sa a maimakon man fetur, tsaftar sa ga muhalli, akwai manyan kalubale masu tsoratarwa wanda suka hada da tsadar aikin sauya war da akalla yaka sama da miliyan Daya, wanda ba kowa ne zai iya biya ba a Najeriya.
Haka Zalika, Wani abin damuwa shine yuwuwar fashewar gas din a cikin mota wanda ke da babban hadari ga rayuwar al’umma da ke ciki da kewayen inda motocin masu iskar gas suke.
Alal misali, a ranar Laraba, 16 ga Oktoba, 2024, wata mota kirar samfurin iskar gas na CNG ta kama da wuta gadan gadan a tashar NIPCO CNG da ke Aduwawa a cikin garin Benin, lamarin da ya haifar da jikkata mutane da dama da asarar dukiyoyi.
Sai dai, bayan jajantawa da tayi, gwamnatin ta zargi masu motar da sauya ta bisa ka’ida ba da bin tsarin gwamnati.
Wata hanya kuma na samun saukin sufuri da gujema amfani da man fetur, tsadar sa da kuma gurbata muhalli da yake, itace motoci masu amfani da wutar lantarki.
Motoci masu amfani da wutar lantarki suna da tsafta saboda masu gurbata muhalli, amma said ai suna da dankaran tsada.
A kokarin gano hanyoyin sufuri mai dorewa; Amfani da Iskar gas samfurin CNG akwai arha matuka a Najeriya, ga kuma motoci masu amfani da lantarki, wanda dukkanin su zabi ne mai matukar kyau, toh amma sai dai dukkanin su suna da dankaran tsada wajen sauyawa ko sayan su.
babbar tambayar ita ce: Shin shirin sauya motoci izuwa amfani da iskar gas Ta CNG ko masu amfani da wutar lantarki za su iya magance tsadar kudun sufuri da ake fama da shi yanzu A Najeriya?