Bayan rantsuwar kama aiki da ake sa ran zai yi a ranar 20 ga Janairu 2025, Donald Trump na fuskantar wani sabon dama domin gudanar da abubuwan da ya yi wa Amurkawa alƙawari a lokacin yaƙin neman zaɓensa.
Ana hasashen cewa Trump zai fara wa'adinsa na biyu a matsayin shugaban ƙasa da zafafan tsare-tsare, tare da karfin rinjaye na jam'iyyarsa ta Republican a majalisar dokokin ƙasar. Waɗannan tsare-tsare sun shafi batutuwan da suka haɗa da shige da fice, tsaron iyaka, gyare-gyare a tattalin arziki, da kuma manufofi na kasashen duniya.
Tsaron Iyaka da Shige da Fice
Ofishin yaɗa labaran Trump ya bayyana cewa shugaban ƙasar
zai aiwatar da wani shirin gaggawa na tabbatar da tsaron iyaka da kuma yaƙi da
matsalar bakin haure. Karoline Leavitt, sakatariyar yaɗa labaransa, ta bayyana
cewa "Trump zai fara aiki da tsarin tsaro mai ƙarfi a kan iyaka tun daga
ranar farko."
Trump ya naɗa Tom Homan, tsohon jami'in hukumar shige da
fice, a matsayin shugaban wannan kwamiti da zai kula da tsare-tsaren tsaron
iyaka. Homan yana da kwarewa a wannan ɓangare, kuma ana sa ran zai taimaka wa
Trump wajen dawo da manufofin tsaro da aka kafa a wa’adinsa na farko. Trump ya
kuma naɗa Kristi Noem, gwamnar jihar South Dakota, don jagorantar tsaron cikin
gida, wanda zai haɗa da korar bakin haure da ke zaune ba bisa ka'ida ba.
Daga cikin abubuwan da Trump zai yi na tsaron iyaka akwai
sake dawo da dokar "Remain in Mexico," wadda ta buƙaci masu neman
mafaka da su jira a Mexico har sai an kammala duba buƙatunsu. Wannan doka ta
gamu da cikas a lokacin gwamnatin Biden, amma Trump na shirin dawo da ita domin
rage yawan bakin haure da ke shiga ƙasar. Bugu da ƙari, Trump ya yi alƙawarin
kawo ƙarshen zama ɗan ƙasa ta hanyar haihuwa - dokar da ta ce duk wanda aka
haifa a Amurka zai kasance ɗan ƙasa, wanda zai buƙaci canje-canje a kundin tsarin
mulki ko amincewa daga majalisun dokokin jihohi.
Tattalin Arziki da Harkokin Kasuwanci
Wani muhimmin bangare na manufofin Trump shi ne sake farfaɗo
da tattalin arzikin ƙasa da rage farashin kayayyakin masarufi. Trump ya bayyana
cewa yana da niyyar ɗaukar matakai da zasu inganta tattalin arzikin ƙasa ta
hanyar aiwatar da manufofin da zasu rage haraji kan ‘yan kasuwa da kuma sauƙaƙe
kasuwanci.
Trump ya kuma yi alƙawarin sanya haraji mai tsanani kan
kayayyakin da ake shigo da su daga kasashen waje, musamman daga China. A
wa’adinsa na farko, ya ɗaga haraji akan kayayyakin China zuwa kashi 25 cikin
100, kuma ya ce zai ɗaga wannan haraji zuwa kashi 60 cikin 100 idan aka sake
zabensa. Wannan ya nuna cewa Trump na da burin ganin masana’antun Amurka sun
samu ƙarfafawa a kan takwarorinsu na kasashen waje. Haka kuma, Trump ya ce zai
sanya harajin kashi 25 cikin 100 kan kayayyakin da ake shigo da su daga Mexico
idan ba su dakatar da kwararar 'yan ta'adda da kwayoyi da ake zargin suna shigo
wa Amurka ba.
Sha'anin Makamashi da Sauyin Yanayi
A matsayin wanda ya sha caccakar manufofin gwamnatin Biden
akan yanayi, Trump ya bayyana cewa zai yi duk mai yuwuwa domin ƙarfafa bangaren
samar da makamashi a Amurka. A yaƙin neman zaɓensa na farko, ya fice daga
yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris, sannan yana sa ran zai ci gaba da wannan
akida idan ya sake zama shugaban ƙasa. Yarjejeniyar ta Paris ta buƙaci ƙasashen
duniya su haɗa kai wajen rage fitar da iskar Carbon da ke cutar da yanayi, amma
Trump ya yi imanin cewa hakan na da illa ga masana’antun Amurka.
Trump ya sha alwashin ba da fifiko ga haƙar mai da iskar gas
da kuma rage takunkumin da aka sanya a kan masana'antun da ke gurbata muhalli.
Ya ce, "Za mu ci gaba da hakowa, hakowa, hakowa," domin samar da
ayyuka da rage dogaro kan kasashen waje. Wannan na nufin cewa zai yi ƙoƙarin
rage ayyukan haɓɓaka makamashi mai tsafta da kuma rage yawan motocin lantarki
kamar yadda gwamnatin Biden ta tsara.
Rasha da Ukraine
Trump ya yi wasu kalamai masu sosa zuciya a kan yaƙin da ke
tsakanin Rasha da Ukraine. A yaƙin neman zaɓensa, ya yi ikirarin cewa zai iya
kawo ƙarshen yaƙin "cikin kwana guda" ta hanyar kawo yarjejeniya
tsakanin bangarorin biyu. Duk da haka, bai bayyana takamaiman yadda zai cimma
hakan ba. Kodayake, ya bayyana goyon baya ga rage tallafin da Amurka ke bai wa
Ukraine, yana mai cewa wannan yaƙi na janyo asarar kuɗaɗe ga Amurka.
A cikin wani lokaci na kwanan nan, Trump ya yi wata magana
ta wayar tarho da shugaban ƙasar Ukraine Volodymyr Zelensky da hamshakin
attajiri Elon Musk, amma wata majiya ta bayyana wa BBC cewa "hirar ba ta
kai ga takamaiman abubuwa ba." Wannan ya nuna cewa Trump na iya ɗaukar
wani matsayi mai rauni ga Ukraine, wanda zai iya shafar alaƙar Amurka da
ƙasashen yammacin Turai masu goyon bayan Ukraine a wannan yaƙi.
Shari'a da Gafara
Trump na da karfi a yankin shari’a kuma yana iya bada gafara
ga wasu mutane da ke fuskantar hukunci ko kuma shari'a dangane da abin da ya
faru a harin da aka kai majalisar dokoki a 2021. Fiye da mutane 1,500 aka kama
saboda laifuka daban-daban na shiga majalisar dokoki ba bisa ka’ida ba, inda
wasu daga cikinsu ke fuskantar hukunci mai tsanani.
Jack Smith, lauya mai shigar da kara na musamman da ke
jagorantar bincike akan Trump dangane da abubuwan da suka faru bayan zaɓen
2020, na cikin masu fuskantar kalubale daga wannan zabi na Trump. Trump ya ce
yana da burin ganin cewa yana iya sallamar Jack Smith ko kuma rage tasirin
binciken da yake gudanarwa.
Sauyin Dokokin Lafiya
Trump ya bayyana cewa zai maido da sauye-sauyen da ya fara a
lokacin wa'adinsa na farko akan Title X, wanda shi ne shirin tallafi na kiwon
lafiya na tarayya. A lokacin wa'adinsa na farko, Trump ya kafa wata doka da ta
haramta bayar da shawarwari kan zubar da ciki ga marasa lafiya da ke karɓar
tallafin gwamnati ta Title X. Wannan mataki ya janyo cikas ga ƙungiyoyi irin su
Planned Parenthood waɗanda suke tallafawa marasa lafiya da ke bukatar wannan
shawarwari.
Shugaba Biden ya janye wannan doka bayan ya hau mulki, amma
yanzu Trump na da niyyar dawo da ita, lamarin da zai iya shafar dubban mutane
waɗanda ke neman tallafin kiwon lafiya.
Cigaba da Tattaunawa Akan Kudade da Kuɗaɗen Crypto
Trump ya sha yin kalamai masu goyon baya ga kasuwar kuɗaɗen
Crypto. Bayan lashe zaɓen, darajar Bitcoin ta ƙaru da kashi 30 cikin 100 cikin
mako guda sakamakon tsammanin cewa gwamnatin Trump za ta goyi bayan harkar kuɗaɗen
Crypto fiye da gwamnatin Biden. Trump ya kuma yi alƙawarin korar shugaban
hukumar kula da kasuwannin hada-hadar hannun jari, Gary Gensler, wanda ya
bayyana niyyarsa ta tabbatar da bayyanar yanayi a harkokin kasuwanci.
Kammalawa
Duk da cewar Trump ya fi kowane tsohon shugaban ƙasa
fuskantar ƙalubale a bangaren shari'a, yana da manufa mai karfi a wa'adinsa na
biyu. Wannan zai ba shi dama na tabbatar da wasu sauye-sauye da suka shafi
fannin shige da fice, tsaro, tattalin arziki, da kuma tsare-tsaren lafiya. Duk
da haka, akwai alamun tambaya kan yadda zai cimma waɗannan manufofi, musamman
duba da yadda za a iya fuskantar ƙalubalen doka daga ɓangaren adawa da ke
fargabar irin matakan da zai dauka a wa’adinsa na biyu.