Hon. Sani Sha'aban Danburan Zazzau, tsohon ɗan Majalisar Wakilai na Tarayyar Najeriya, ya yi wa Muryar Amurka karin bayani mai zurfi kan manyan matsalolin da suka addabi yankin Arewa. A cikin hirar, ya bayyana yadda rashin tsaro, ƙarancin ilimi, talauci mai tsanani, da kuma rashin isassun ababen more rayuwa suka kasance manyan ƙalubale da ke ci gaba da dagula rayuwar al’umma a yankin.
Hon. Sani Sha'aban ya kuma fayyace hanya guda da ya ke ganin ita ce mafita ga wadannan matsaloli masu tsanani, yana mai jaddada cewa akwai bukatar haɗin kai tsakanin gwamnati, al'umma, da masu ruwa da tsaki don kawo sauyi mai dorewa. Ya yi tsokaci kan yadda inganta ilimi, karfafa sana'o'in hannu, da samar da ababen more rayuwa na zamani za su iya magance talauci da kuma rage tasirin rashin tsaro da ya zama babbar barazana ga ci gaban yankin Arewa.
A wannan tattaunawa ta musamman, Hon. Sani Sha'aban ya nuna damuwarsa kan halin da ake ciki, tare da kira ga gwamnati da al'ummar yankin su farka domin su yi aiki tare wajen gina makoma mai kyau. Wannan hirar ta kawo cikakken haske kan irin rawar da shugabanni irin sa za su iya takawa wajen kawo ci gaba mai ma'ana ga Najeriya baki ɗaya