API

Koyon Yadda Ake Karatun Hausa Da Rubutun Hausa A Saukake

Wannan littafi mai kayatarwa, "Koyon Karatun Hausa a Sauƙaƙe", wanda marubucinsa shi ne Yusuf Aminu, wanda aka fi sani da Yusufuddeen A. Yusuf. Wannan littafi na musamman ya kasance cikakken jagora ga masu koyon harshen Hausa, musamman waɗanda ke son koyon karatu da rubutu cikin sauƙi.



Game da Littafin

Littafin ya ƙunshi darussa masu sauƙi da kuma labarai masu kayatarwa waɗanda ke taimakawa wajen fahimtar tsarin haruffa da rubutun Hausa. An tsara shi ne domin ya dace da masu farawa da kuma masu son ƙwarewa a harshen Hausa. Har ila yau, littafin yana ɗauke da:


  • Haruffan Hausa da yadda ake amfani da su.
  • Misalai na kalmomi da jimloli domin yin rubutu.
  • Labarai masu nishaɗi da darasi don inganta karatun Hausa.
  • Koyarwa kan haruffa masu lankwasa da dabarun amfani da su.

Darasi Na Biyu: 

Game da Marubucin

Yusufuddeen A. Yusuf ɗan jarida ne na dijital, mai ƙwarewa a fannin shirya bidiyo, rubuce-rubuce, da koyar da dabarun fasaha ta dijital. Ya samu gogewa daga manyan kwararrun ma'aikata na gidajen watsa labarai kamar Muryar Amurka (VOA Hausa), DW Hausa, da BBC Hausa. A halin yanzu, yana bayar da tallafin koyon dabaru kyauta ta tashar YouTube ɗinsa mai suna YDEEN NETWORKS, inda yake da mabiya sama da 305,000 a dandalin zamani.


Abin da Zai Amfanar da Kai a Wannan Littafi

  • Wannan littafi zai taimaka wa yara, matasa, da manya wajen koyo da koyar da harshen Hausa cikin sauƙi.
  • Zai ƙara wa malamai dabaru wajen koyar da harshen Hausa a makarantu.
  • Masu sha’awar rubutun Hausa za su koyi yadda za su inganta fasaharsu ta rubutu da sadarwa

Yadda Za a Samu

Za'a iya sauke littafin a link da ke kasa kuma za a iya karantawa kyauta. A matsayinka na mai sha’awar harshen Hausa, wannan littafi zai taimaka maka wajen samun ilimi mai amfani da kuma fahimtar karatu da rubutun Hausa da kyau.



Koyon Yadda Ake Karatu Da Rubutun Hausa A Sauƙaƙe

Danna wannna link domin sauke >> KOYON KARATU DA RUBUTUN HAUSA A SAUKAKE