Labarin matashiya Sumayya wacce aka fi sani da Aisha Mohammed Buba Mashio wacce ta shahara a zane-zane tare da labarin sauran 'yan uwanta matasa.
Matasan daga arewacin Najeriya sun bayyana tarihi da labarin rayuwar su da yadda suka gano suna da basira da hikima ta zane-zane, da kuma irin gudun mawar da suka baiwa al'umma dalilin sana'ar tasu.
Haka zalika sun bayyana irin kalubale da suke fuskanta a sana'ar ta su, ga cikakken rahoton na bidiyo a kasa.