Farfesa Ibrahim Gambari, tsohon mai ba da shawara na musamman ga Majalisar Dinkin Duniya, ya bayyana damuwa kan yadda rashin tsaro ke addabar kasashen Afirka. Ya ce lokaci ya yi da shugabannin nahiyar za su dauki matakan gaggawa domin magance matsalolin Boko Haram, 'yan bindiga, da masu garkuwa da mutane.
Ya yi gargadin cewa rashin daukar matakan da suka dace na
iya kara haifar da durkushewar tattalin arziki da kuma karuwar talauci.