Yan tawaye masu fafutikar dawo da gwamnatin Mohamed Bazoum sun ajiye makamai, suna neman zaman lafiya a Nijar
A Jamhuriyar Nijar, mayakan ƙungiyar Front Patriotique de Libération (FPL), masu fafutikar dawo da gwamnatin Mohamed Bazoum da sojoji suka kifar, sun ajiye makamai tare da mika wuya. Wani biki na musamman aka shirya a fadar gwamnatin Agadez a arewacin kasar domin karrama wannan mataki na zaman lafiya.
Mahmoud Salah, tsohon ɗan tawaye da ya taba tuba, ya jagoranci wannan ƙungiya ta FPL. A cikin makon da ya gabata, wasu manyan jiga-jigan ƙungiyar, ciki har da kakakin ƙungiyar, Idrissa Madaki, tare da wasu kwamandoji uku, sun bar fafutika. Sun bayyana cewa sun yanke shawarar rungumar zaman lafiya, suna mai nuna muhimmancin tsaro da kwanciyar hankali ga Nijar da ma yankin arewacin kasar baki daya.
A baya, ƙungiyar FPL ta kasance a sahun gaba wajen kai hare-hare da ke haddasa rashin tsaro a Nijar, har ma ta kaddamar da hare-hare kan bututun danyen mai da kuma ta yi garkuwa da kantoman Bilma a arewa. Wannan sabon mataki na mika wuya da rungumar zaman lafiya ya kawo sabon fata ga Nijar da neman inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.