API

Donald Trump Ya Karɓi Rantsuwar Kama Aiki: Sabon Shugaban Amurka na 47

A ranar Litinin, 20 ga Janairu, 2025, Donald John Trump ya karɓi rantsuwar kama aiki a matsayin Shugaban Amurka na 47, bayan nasarar da ya samu a zaɓen watan Nuwamba na bara. An gudanar da bikin rantsarwa a fadar White House, inda mataimakinsa, JD Vance, ya fara karɓar rantsuwa kafin Trump.



Bayan rantsarwa, Shugaba Trump ya bayyana shirin fitar da jerin umarnin zartarwa don magance matsalolin ‘yan ƙasa da bakin haure. Ya ce zai ayyana dokar ta-baci a kan iyakar kudu da Amurka, tare da tura dakarun soja domin dakile shigowar bakin haure ba bisa ƙa’ida ba. Haka kuma, ya yi alkawarin mayar da miliyoyin bakin hauren da suka aikata laifuka zuwa kasashensu na asali.



Trump ya kasance shugaban Amurka na farko da aka taɓa samu da laifi kafin ya hau mulki. A bara, wata kotu ta same shi da laifuka 34 masu nasaba da shirya bayanan kasuwanci na bogi, domin ɓoye biyan kuɗi dala 130,000 ga wata jarumar fina-finan batsa, Stormy Daniels. Duk da haka, alkalin kotun ya ƙi yarda ya yanke masa hukunci na ɗaurin kurkuku.