Kasa da mako guda bayan fashewar da ta afku a bututun mai na Trans Niger Pipeline da ke Bodo, ƙaramar hukumar Gokana a Jihar Rivers, wani sabon fashewa ya sake afkuwa a wurin samar da man fetur na Soku da ke ƙaramar hukumar Akuku Toru.
Kungiyar Youths and Environmental Advocacy Centre (YEAC-Nigeria), wata ƙungiya mai rajin kare muhalli a yankin Niger Delta, ta tabbatar da afkuwar wannan fashewa a ranar Lahadi.
A cikin wata sanarwa da shugabanta, Dakta Fyneface Dumnamene Fyneface, ya sanya wa hannu, YEAC ta bayyana cewa ta samu rahotanni daga matasa masu sa ido a yankin kan fashewar da ta afku da safiyar Lahadi a wurin hakar mai na Soku, wanda kamfanin Nigeria Liquefied Natural Gas (NLNG) Limited ke kula da shi.
Sanarwar ta ce: “Wata fashewa da ta kasance tare da harshen wuta an ji karar ta kuma an hango ta daga sararin samaniya daga yankin wurin, wanda da kyar ake iya isa wajen. Har zuwa lokacin da muke bayar da wannan rahoto, wutar na ci gaba da ruruwa.”
Har yanzu ba a tantance musabbabin fashewar ba, sai dai ana hasashen dalilai kamar:
• Gazawar kayan aiki
• Harin ta’addanci
Wannan shi ne karo na uku da ake samun fashewa a wuraren hakar mai a Jihar Rivers a cikin ƙasa da mako guda. Fashewar farko ta afku a Ogoni, yayin da ta biyu ta faru a ƙaramar hukumar Ogba/Egbema/Ndoni – lamarin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ambata a jawabin da ya gabatar wa ƙasa a ranar 18 ga Maris, inda ya ayyana dokar ta-ɓaci na tsawon watanni shida a jihar Rivers.