Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana cewa ba a tabbatar ko zai sake tsayawa takarar shugabancin ƙasar a zaɓen 2027 ba. Atiku ya yi wannan bayani ne a wata hira da gidan talabijin na Arise, inda aka saki wani ɓangare na tattaunawar a ranar Laraba.
A cikin hirar, an tambayi tsohon mataimakin shugaban ƙasar game da shugabancin haɗakar da ’yan adawa ke shirin kafawa, sai ya kwatanta hakan da irin yadda aka kirkiro jam’iyyar APC a baya, inda bayan zaɓen fitar da gwani, sauran ‘yan takara suka haɗa kai domin mara wa mutum ɗaya baya har ya yi nasara a babban zaɓe.
Lokacin da aka tambaye shi ko zai sake tsayawa takara, sai Atiku ya ce: “Ban sani ba, domin ya kamata a samar da tsari mai inganci tukuna.”
A makon da ya gabata, Atiku ya bayyana cewa jam’iyyun adawa a Najeriya na tattaunawa kan yadda za su haɗa kai domin fuskantar jam’iyya mai mulki a zaɓen 2027. Idan ana tuna wa, Atiku Abubakar ne ya zo na biyu a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, inda Bola Ahmed Tinubu ya samu nasara.
Tun bayan hawansa mulki, ana ci gaba da fuskantar ƙalubale na tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar. Masana harkokin siyasa da tattalin arziki na danganta hakan da manufofin gwamnatin Tinubu, musamman cire tallafin man fetur da kuma barin kasuwa ta tantance darajar kuɗin ƙasashen waje, wanda hakan ya haddasa faduwar darajar naira.