Nasir El-Rufa'i Ya Bayyana Dalilin Ficewarsa Daga APC
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i, ya tabbatar da ficewarsa daga jam'iyyar APC, yana mai bayyana cewa ya koma jam’iyyar Social Democratic Party (SDP).
A ranar Litinin, 10 ga Maris, 2025, El-Rufa'i ya wallafa a shafukan sada zumunta cewa ya ajiye katin zama dan jam’iyyar APC a mazaɓarsa da ke Kaduna. Ya ce tun kafin yanke wannan hukunci, ya tattauna da magoya bayansa da abokan tafiyarsa a fadin Najeriya, kuma ya yanke shawarar ci gaba da siyasa a karkashin SDP.
Dalilan Ficewa Daga APC
A baya-bayan nan, El-Rufa’i ya bayyana rashin jin dadinsa kan yadda APC ke tafiyar da al'amuranta, yana mai cewa jam’iyyar ta kauce daga akidunta na asali.
"Abubuwan da suka faru cikin shekaru biyu da suka wuce sun tabbatar da cewa shugabannin jam’iyyar ba su da niyyar magance matsalolin da suka addabi APC," in ji shi.
Ya bayyana cewa ya yi ƙoƙarin jawo hankalin manyan jam’iyyar a ɓoye da kuma a fili kan halin da ake ciki, amma ba a saurare shi ba. Saboda haka, ya ce dole ya nemi mafita a wata sabuwar jam’iyya da za ta dace da manufofinsa.
El-Rufa’i Da APC
El-Rufa’i ya tunatar da irin gudunmawar da ya bayar wa APC tun kafuwarta har zuwa nasarorin da jam'iyyar ta samu a zaɓukan 2015, 2019 da 2023. Sai dai ya ce a halin yanzu jam’iyyar ta sauya salo, ta juya wa mabiyanta baya kuma ba ta mutunta manufofinta na farko.
Ya kuma zargi shugabannin APC da kasa gudanar da taron shugabannin jam’iyyar na ƙasa tsawon shekaru, abin da ya ce ya sabawa dokokin kundin tsarin jam’iyyar.
Meyasa SDP?
El-Rufa’i bai fayyace ainihin dalilin da ya sa ya zabi SDP ba, amma ya bayyana cewa jam’iyyar ce mafi kusa da manufofinsa na kawo ci gaba a Najeriya. Har ila yau, yana da kyakkyawan fata kan makomar siyasar sa a cikin SDP.
Tun bayan da majalisar dattijai ta hana tantance shi don nadin mukami a gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, masu lura da siyasa sun dade suna nazari kan matakin da tsohon gwamnan zai dauka. Wannan matakin na El-Rufa’i ya kawo karshen rade-radin da ake yi kan makomarsa a siyasa.
Ko da yake a baya El-Rufa’i ya ce zai koma harkokin karatu da rayuwa ta sirri bayan wa’adinsa na gwamna, da alama siyasar ta sake ja da shi zuwa wani sabon fagen gwagwarmaya a karkashin SDP.