Niamey, Nijar – 22 ga Maris, 2025
Gwamnatin sojin Jamhuriyar Nijar ta ayyana zaman makoki na kwanaki uku bayan wani mummunan harin ta'addanci da ya yi sanadin mutuwar mutane 44 a kauyen Kokorou, kusa da iyakar Burkina Faso da Mali. Rahotanni sun bayyana cewa, maharan sun kai harin ne a Masallacin Juma'a na unguwar Fambita, inda suka kewaye masallacin dauke da muggan makamai, suka kashe mutane 44, tare da jikkata wasu 13.
Bayan kisan, 'yan ta'addan sun kona kasuwar garin da gidaje, lamarin da ya haifar da asarar dukiya mai yawa. Gwamnatin Nijar ta yi alkawarin kamo 'yan ta'addan da suka aikata wannan ta'asa, tare da tabbatar da cewa za a hukunta su yadda ya dace.
A halin yanzu, an tura jami'an tsaro zuwa yankin domin tabbatar da tsaro da kuma taimakawa al'ummar da abin ya shafa.
Gwamnati ta kuma bukaci al'umma da su kasance masu lura da tsaro, tare da ba da hadin kai ga hukumomi wajen yaki da ta'addanci.
Ana sa ran gudanar da addu'o'i na musamman a fadin kasar domin neman zaman lafiya da kwanciyar hankali.