API

Janar Abdourahamane Tchiani Ya Zama Shugaban Riƙon Ƙwarya na Nijar na Shekaru 5

A ranar Laraba, an rantsar da shugaban mulkin sojan Nijar, Janar Abdourahamane Tiani, a matsayin shugaban riƙon ƙwarya na ƙasar har tsawon shekaru biyar. Wannan mataki ya biyo bayan wata sabuwar yarjejeniya da ta maye gurbin kundin tsarin mulkin Nijar, wanda hakan ke nuna wa’adin mulkin sojoji kafin miƙa iko ga farar hula.

Mahamane Roufai, Sakatare-Janar na gwamnatin Nijar, ya bayyana cewa wannan sabon wa’adin ya fara aiki daga ranar Laraba, a yayin wani biki da aka gudanar a Yamai, babban birnin ƙasar. Wannan na zuwa ne bayan wani taron ƙasa da aka gudanar kwanan nan, wanda ya amince da wannan sabon tsari na miƙa mulki.





Kazalika, gwamnatin sojan Nijar ta ɗaga martabar Abdourahamane Tiani daga matsayin Birgediya Janar zuwa Janar, wanda shi ne muƙamin soja mafi girma a ƙasar. Wannan ƙarin matsayi na ƙara tabbatar da ikon da Tiani ke da shi, tun bayan jagorantar juyin mulkin da ya kifar da gwamnatin farar hula a watan Yulin 2023.


Matakin na Nijar ya saɓa da buƙatar ƙungiyar ECOWAS wacce ke matsa lamba kan gaggauta dawo da mulkin dimokuraɗiyya a ƙasar, bayan juyin mulkin da ya kawo ƙarshen gwamnatin da aka zaɓa ta dimokuraɗiyya.