Wannan ƙuduri, wanda ɗan majalisa Solomon Bob ya dauki nauyinsa, ya tsallake karatu na biyu tare da wasu ƙuduroi 41 a zauren majalisa a ranar Laraba. An mika shi zuwa kwamitin majalisar kan sauya tsarin mulkin ƙasar don ci gaba da aiki a kansa.
Bob ya bayyana cewa manufar dokar ita ce ƙarfafa gaskiya da riƙon amana a shugabanci ta hanyar cire kariya daga waɗanda ke rike da manyan mukamai, don hana cin hanci da rashawa da kuma dakile rashin hukunci.
Dokar tana da nufin gyara sashe na 308 na kundin tsarin mulkin ƙasar na shekarar 1999, wanda ke baiwa shugaban ƙasa, mataimakin shugaban ƙasa, gwamnoni da mataimakansu kariya daga gurfanarwa a gaban kuliya a lokacin da suke rike da mukamansu. Idan aka amince da wannan ƙuduri gaba ɗaya, kawai shugaban ƙasa ne zai ci gaba da samun wannan kariya, yayin da sauran manyan jami’an gwamnati za su iya fuskantar shari’a idan an zarge su da aikata laifi.
Wannan mataki na majalisa yana ɗaya daga cikin gyare-gyaren da ake yi a kundin tsarin mulkin ƙasar domin tabbatar da an dakile rashin hukunci a tsakanin shugabanni, tare da ƙarfafa doka da oda.
Duk da haka, kafin ƙudurin ya zama doka, sai majalisar dattawa ta amince da shi, sannan a miƙa shi ga shugaban ƙasa domin ya rattaba hannu.