API

Shugabar Matan APC ta Kaduna Ta Janye Goyon Bayan El-Rufai, Ta Marawa Uba Sani Baya

Shugabar matan jam’iyyar APC a Jihar Kaduna, Maryam Suleiman, ta janye goyon bayanta ga tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, tare da bayyana cikakken goyon bayanta ga gwamna mai ci, Uba Sani.

Maryam, wacce aka sani da kasancewa a hannun daman El-Rufai, ta bayyana cewa sauya sheƙar tsohon gwamnan zuwa jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) ba shi da wata fa’ida a siyasance.



A baya, an dakatar da ita daga jam’iyyar APC sakamakon sukar da ta yi wa Gwamna Uba Sani. Sai dai yanzu, ta bayyana nadama kan furucinta, tana mai cewa maganganunta a baya sun kasance sakamakon ‘bacin rai na yara’.

A yayin wata tattaunawa da manema labarai, Maryam ta bayyana cewa Gwamna Uba Sani shugaba ne mai tausayi kuma ya riga ya yafe mata. Ta kara da cewa a lokacin da ta yi suka, ba ta fahimci abubuwan da ke faruwa ba, amma yanzu ta gane kuskurenta kuma ta ba da hakuri.

Ta kuma bayyana cewa gwamnatin El-Rufai ta yi kurakurai da dama, musamman wajen rusa kasuwanni da korar malaman firamare.

Maryam ta tabbatar da cewa har yanzu tana cikin APC, kuma ba za ta sauya sheƙa zuwa wata jam’iyya ba, domin ita ‘yar asalin jam’iyyar ce.