API

Sule Lamido Ya Mayar Da Martani Kan Kiran El-Rufai Na Sauya Sheƙa Zuwa SDP

Tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma jigo a jam’iyyar PDP, Alhaji Sule Lamido, a wata hira da BBC-Hausa ya mayar da martani mai zafi kan tayin da tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya yi wa manyan 'yan siyasa da su bi sahunsa zuwa sabuwar jam’iyyarsa ta SDP.

A makon da ya gabata ne El-Rufai ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC zuwa SDP, yana mai kiran wasu jiga-jigan siyasa, ciki har da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, Peter Obi, Rotimi Amaechi, da Rauf Aregbesola, da su sauya sheƙa zuwa SDP.

Sai dai Sule Lamido ya caccaki wannan kira, yana mai bayyana cewa El-Rufai ba shi da wata akidar siyasa ta ci gaba da kishin al'umma da har zai yi wa PDP tayin canza sheƙa zuwa SDP.



"Ba El-Rufai Zai Fadawa 'Yan PDP Su Sauya Sheƙa Ba"

A cewarsa, "Yanzu ba don raini ba, saboda Allah, ya zai kalle mu a PDP ya ce zai kira mu wata jam’iyyar siyasa? Jam’iyyar da muka yi ta PDP ita ce ta haife shi."

Lamido ya kara da cewa El-Rufai ya taɓa bayyana cewa babu manya a siyasar Najeriya, amma yanzu yana neman jawo su PDP zuwa sabuwar jam'iyyarsa.

"Amma ya wayi gari ya ce ya fadawa Buhari, yanzu ai ba za ka kalle ni ka ce na bi umarnin Buhari ba, idan dai har haka ne bai kamata ya je wajen Buhari ba tun da ya ce su ne manya," in ji Sule Lamido.

Lamido, wanda ya taba zama sakataren jam'iyyar SDP a baya, ya ce bai ga wata matsala da PDP ba kuma yana nan daram a cikinta.

"Duk rikicin da PDP take ciki, a nan aka haife shi (El-Rufai). Idan ya ce PDP ta mutu to a nan ne asalinsa, nan ne aka haife shi," in ji shi.

"Ba A Iya Kada Tinubu Cikin Fushi"

Lamido ya ce idan da har zai bar PDP, da tun lokacin da aka kafa hadakar APC a 2014 ya fice, amma ya tsaya daram a PDP.

Ya bayyana cewa ana korafin APC ta gaza, kuma tun farko yana daga cikin masu sukar jam’iyyar. A cewarsa, shugabanci ba a yinsa cikin fushi da haushi, sai da hangen nesa da kishin kasa.

"Idan ka ce za ka yi amfani da fushinka don biyan wata bukata, ba za ka taba hukunci kan kasa ba sai don son ranka."

Lamido ya jaddada cewa idan ana so a yi wa Najeriya gyara, dole a sa kishin kasa a gaba, ba wai a yi tafiya da fushi da mutum daya ba.

"A yi tafiyar ne domin nuna cewa kasa ba ta tafiya daidai, sannan a gyara inda aka samu matsala wajen tabbatar da adalci da zaman lafiya," in ji Sule Lamido.