API

’Yan Bijilanti A Edo Sun Kashe Mafarauta ’Yan Arewa a Hanyar Jihar Rivers

A Jihar Edo da ke Kudu maso Kudu, wasu ’yan bijilanti sun hallaka mafarauta 27 daga Arewacin Najeriya yayin da suke kan hanyarsu ta dawowa gida daga Jihar Rivers.


Rahotanni sun bayyana cewa 25 daga cikin maharba da aka kashe ’yan asalin Jihar Kano ne, yayin da biyu suka fito daga Jihar Katsina. Wannan harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 21, yayin da aka kwantar da biyar a asibiti domin samun kulawar gaggawa.



Wannan mummunan kisa ya haifar da cece-kuce daga bangarori daban-daban, ciki har da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, da tsohon Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, wadanda suka bukaci a gudanar da bincike mai zurfi domin tabbatar da adalci.


Ana danganta wannan hari da jerin cin zarafin da wasu ’yan Arewa ke fuskanta a wasu sassan Kudancin Najeriya, wanda a lokuta da dama ke haddasa saɓani da rashin jituwa tsakanin yankunan kasar.


x