API

’Yan Sanda Sun Haramta Bukukuwan Hawan Sallah a Kano

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta hana duk wani biki na Hawan Sallah (Durbar) yayin bukukuwan Eid-El-Fitr na 2025, bisa dalilan tsaro da bukatar tabbatar da zaman lafiya a fadin jihar. Kwamishinan ’Yan Sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ne ya sanar da matakin yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar rundunar da ke Bompai a ranar Juma’a.



Ya bayyana cewa, bayan gudanar da cikakken binciken tsaro, an gano barazanar tashin hankali da wasu gungun bata-gari ke shirin haddasawa ta hanyar amfani da bukukuwan Hawan Sallah.


“Mun samu sahihan bayanan sirri kan shirin wasu bata-gari da masu daukar nauyinsu, wadanda ke da niyyar amfani da Hawan Sallah domin tayar da zaune tsaye. Bisa haka, rundunar ’yan sanda, tare da hadin gwiwar Gwamnatin Jihar Kano da sauran masu ruwa da tsaki, ta yanke shawarar hana duk wani biki na Hawan Sallah a jihar,” in ji CP Bakori.


Kwamishinan ya tabbatar wa da al’ummar Kano cewa an dauki duk matakan da suka dace domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya yayin bukukuwan Sallah.


Ya kuma bukaci jama’a da su bi ka’idojin tsaro, ciki har da gujewa daukar duk wani abu da zai iya haddasa zargi, tare da haramta hawa dawakai (Kilisa), tseren motoci, da tukin ganganci.