API

Gwamnatin Nijar Ta Zabi Hausa A Matsayin Harshe Na Kasa

Faransanci Da Ingilishi Zasu Kasance Harsunan Aiki

Gwamnatin mulkin soja ta Jamhuriyar Nijar ta bayyana Hausa a matsayin harshe na kasa, yayin da Faransanci da Ingilishi suka zama harsunan aiki a hukumance.

A cikin kudiri mai lamba 12 na kundin tsarin mulkin rikon kwaryar kasar ta Nijar, an sanar da cewa Hausa zai kasance harshen da aka dauka a matsayin na kasa baki daya, inda kuma Faransanci da Ingilishi za su kasance harsunan aiki na gwamnati. Wannan mataki na musamman ya bayyana bayan tattaunawa mai zafi da kuma muhawara a shafukan sada zumunta kan matsayar da za a dauka kan harshen da ya kamata a zabi a matsayin na kasa.



A cikin wannan sabuwar dokar, an bayyana cewa harsunan da ake amfani da su a Nijar sun hada da Larabci, Buduma, Fulatanci, Gurmanci, Hausa, Kanuri, Tagdalci, Tamajaq, Tassawaq, Tubanci da Zabarmanci. Sai dai, bisa ga yadda Hausa take yaduwa a fadin kasar, wannan harshe ya samu matsayi na musamman na zama harshe na kasa, yayin da Faransanci da Ingilishi za su ci gaba da kasancewa harsunan da ake amfani da su a cikin hukumomi da mu'amalar gwamnati.

Bari Arzika, wani dan jarida da masanin kimiyyar harsuna, ya bayyana cewa, "Hausa ba wai harshe ne na kabilar Hausawa kawai ba, har ma da sauran kabilu a Nijar suna amfani da shi." Ya kara da cewa, wannan mataki na baiwa harsunan gida mahimmanci yana nufin inganta darajar su, wanda zai taimaka wajen gina al'umma da kuma tabbatar da hadin kai a tsakanin kabilu.



Hakan ya kawo tambaya mai muhimmanci ga wasu masu kallon sabuwar dokar, musamman yadda al'ummar da suka saba da amfani da harsunan waje za su dauki wannan mataki da zai inganta amfani da harsunan gida a mu'amala ta yau da kullum. A halin yanzu, al'ummar Nijar suna ci gaba da tattaunawa game da wannan sauyi mai muhimmanci.