Gwamnonin na Arewa Maso Gabas Sun Roki Sun Roki Shugaba Tinubu Da Ya kammala Hanyoyi 17 da Kuma Binciken man Fetur
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya jagoranci tawagar gwamnonin Arewa maso Gabas wajen ganawa da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a ranar Laraba.
Taron wanda aka yi a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, ya mayar da hankali kan muhimman matsalolin da suka shafi yankin Arewa maso Gabas, musamman kammala gaggawar hanyoyi 17 da ake ginawa da kuma ci gaba da binciken man fetur a rijiyoyin Kolmani da Tafkin Chadi.
Sauran gwamnonin da suka halarta sun haɗa da Muhammadu Inuwa Yahaya na Gombe, Bala Muhammad na Bauchi, Mai Mala Buni na Yobe, Ahmadu Umaru Fintiri na Adamawa da Agbu Kefas na Taraba.
A jawabinsa, Zulum wanda shi ne shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa maso Gabas, ya roƙi shugaban ƙasa da ya kammala ayyukan hanyoyi da ake yi, tare da gina wasu manyan hanyoyi da za su haɗa jihohin yankin guda shida.Hanyoyin sun haɗa da: Kano–Maiduguri, layin dogo na Port Harcourt–Jos–Bauchi–Maiduguri, Bama–Mubi–Yola, Wukari–Jalingo–Yola, Duguri–Mansur (aikin NNPC na gudana), Bauchi–Gombe–Biu–Damaturu, Damaturu–Geidam, Bauchi–Ningi–Nasaru–Babaldo, da kuma Gombe–Potiskum–Damaturu–Biu.
Sauran hanyoyin sun haɗa da: Alkaleri–Futuk, Maiduguri–Damboa–Yola, Gombe–Dukku–Darazo, Biu–Gombe, Ibi–Shamdam, Maiduguri–Monguno–Baga da Maiduguri–Ngala–Bama–Banki.
Gwamna Zulum ya yaba wa shugaban ƙasa bisa jajircewarsa wajen dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas, inda ya ce:
“Mun gode maka da ka ƙara ƙarfafa zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankinmu, tare da ci gaba da manufofin wanda ya gabace ka wajen yaƙar ta’addanci.”
Ya kuma tabbatar da cewa su, a matsayinsu na gwamnonin yankin, za su ci gaba da goyon bayan manufofin shugabancin Tinubu wajen horas da ma’aikata da samar da fasaha domin magance matsalar tsaro a dazuka, tare da inganta noma bisa tsarin sabuwar manufa ta samar da abinci.
Ya ce: “Shugaban ƙasa, mu gwamnonin Arewa maso Gabas muna girmama ka, kuma dukkanmu mun amince da yin haɗin kai da kai wajen aiwatar da kyakkyawan mulki ga Najeriya, domin barin tarihi mai kyau da abubuwan tunawa ga ƙasar nan.”
Shugaba Tinubu a martaninsa ya amince da damuwar gwamnonin, tare da tabbatar musu da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kula da bukatun ci gaban yankin Arewa maso Gabas.
Daga lado Salisu M Garba
(VOA Hausa Reporters)