Mazauna unguwar Dorayi Chiranci a cikin birnin Kano sun shiga matsanancin firgici da tashin hankali bayan rahotannin kisan wata matar aure tare da ‘ya’yanta uku a cikin gidansu.
Rahotanni sun nuna cewa wasu da ake zargin tsageru ne, waɗanda har yanzu ba a gano ko su waye ba, sun shiga gidan matar inda suka kashe ta tare da ‘ya’yanta uku. Bayan haka, an bayyana cewa an jefa jaririnta cikin wata rijiya da ke cikin harabar gidan.
Mutanen yankin sun bayyana lamarin a matsayin abin firgici da ban tsoro, inda suka ce irin wannan mummunan aiki ba kasafai ake ganin irinsa ba a yankin. Wasu daga cikin mazauna unguwar sun bayyana alhininsu da fargaba kan asarar rayukan, tare da nuna damuwa kan tabarbarewar tsaro.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a tantance ainihin lokacin da kisan ya faru ba, haka kuma ba a bayyana dalilin aikata wannan ta’asa ba. Lamarin ya jefa yankin cikin yanayin fargaba, inda mazauna suka fara ɗaukar matakan kariya domin kare kansu.
Rahotanni sun kuma nuna cewa tun daga ranar Talata da ta gabata, an fara samun zaman dar-dar a unguwar Dorayi Chiranci sakamakon fargabar sake aukuwar irin wannan lamari.
Mazauna yankin sun yi kira ga hukumomin tsaro, musamman Rundunar ‘yan sandar jihar Kano da su ƙara yawan sintiri da tsaurara matakan tsaro a yankin, tare da tabbatar da an gano tare da cafke waɗanda suka aikata laifin domin su fuskanci hukunci.
Ƙoƙarin jin ta bakin rundunar ‘yan sanda ya ci tura, domin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, bai samu damar amsa kiran waya ba a lokacin tattara wannan rahoto.
Lamarin ya bar al’umma cikin alhini da damuwa, tare da ƙara jaddada buƙatar ɗaukar matakan gaggawa na inganta tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
